Nazari Da Sharhin Waƙar Begen Annabi (S.A.W.) Ta Kabiru Yahaya Classic

    Tsakure

    Sunan maƙalar ‘Nazari da Sharhin Waƙar Begen Annabi (S.A.W.) ta Kabiru Yahaya Classic. A cikin maƙalar an yi sharhin babba da ƙananan saƙonni da waƙar ke ɗauke da su da suka haɗa da yabon Annabi (S.A.W.) da ƙanana irin yabo kan asali da kyauta da jaruntaka da sauransu. Haka kuma an fito da salailai daban-daban da aka tsinta a cikin waƙar gwargwadon fahimta. Daga cikin salailan da aka kawo akwai salon share fage da na buɗe waƙa da salon addu’a da na kamancen fifiko tare da na kasawa da aron kalmomi da tsakuren nassi da salon amshi domin waƙar mai amshi ce da kuma salon rufewa. A taƙaice abubuwan da maƙalar ta ƙunsa ke nan da bayanai da misalan da suka biyo na kowane abu da aka ambata a cikin maƙalar.

    DOI: www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.003

    author/Dano Balarabe Bunza (PhD)

    journal/Zauren Waƙa 4(2) | July 2025 |

    Pages