Dabarun Jawo Hankali a Waƙar ‘Yandotan Tsahe Alhaji Aliyu Ta Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

    Tsakure

    Makaɗan baka na Hausa sun karkasu dangane da rukunan mutanen da suke yi wa kiɗa da waƙa. Waɗannan rabe-rabe na makaɗan baka sun haɗa da makaɗan fada-wato waɗanda suke yi wa fadar sarauta da jami’anta kiɗa da waƙa. Sai kuma makaɗan game-gari, waɗanda suke yi wa sauran jama’a kiɗa da waƙa. Wannan kasona makaɗan game-gari ya haɗa da makaɗan attajirai da masu sana’a da ‘yan siyasa da makaɗan bandariya da na bege da sauransu. Dukkanin waɗannan makaɗa suna amfani da dabarun jawo hankali domin isar da saƙonsu cikin sauƙi da burgewa ga jama’a. Sukan yi hakan ne kuwa domin kwarzanta wanda suke yi wa kiɗa da waƙa, a ɗaya ɓangaren kuma su kushe abokan adawar waɗanda suke wa waƙar. Irin waɗannan dabarun jawo hankali sun haɗa da: kwatantawa wadda ta ƙunshi kamantawa da siffantawa da kuma jinsintarwa. Haka kuma makaɗan sukan yi amfani da dabbantarwa da alamtarwa da sauran dabarun jawo hankali. Wannan takarda ta taƙaita ne ga nazarin siffantawa a cikin waƙar ‘Yandotan Tsahe ta Alhaji Musa Ɗankwairo. Manufar wannan takarda ita ce, bin diddigi tare da bayyana wuraren da Ɗankwairo ya yi amfani da siffantawa a cikin wannan waƙa da kuma hikimomin da suke tattare da yin hakan. Hanyoyin nema da tattara bayanan bincike su ne sauraron waƙoƙin Ɗanƙwairo a faya-fayan C.D da sauran su.

    DOI: www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.004

    author/Babangida Magaji Isa PhD

    journal/Zauren Waƙa 4(2) | July 2025 |

    Pages