Tsakure
Shigowar baƙin al’adun Indiyawa da Turawa ga al’ummar Hausawa ya haifar da sauye-sauye masu ɗinbin yawa ga waƙoƙin ƙarni na 21. Wannan dalili ya sa manazarta ke ƙoƙarin fito da sababbin sigogin da aka gano. Saboda haka babban manufar wannan takarda shi ne, nazarin wasu waƙoƙin ƙarni na21 don fito da sabo salo na taƙaddama. A yayin gudanar da wannan nazari an yi amfani da hanyar Yahya (2001). Takardar ta bayyana cewa taƙaddamar soyayya na daga cikin manyan sauyi da aka samu, kuma taƙaddamar ta kasu gida uku; farar taƙaddama da baƙar taƙaddama da taƙaddama mai dungu. Kuma takardar ta gano cewa kowanne daga ciki ta kasu gida biyu dangane da jinsi, wato ta taƙaddamar maza da ta mata.
DOI: www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.005
author/Ahmed S. Baffa & Ogah Mu. Ibrahim
journal/Zauren Waƙa 4(2) | July 2025 |