Salon Sakaɗe a Waƙoƙin Baka na Hausa: Duba Cikin Wasu Shahararrun Waƙoƙin Mashahuran Mawaƙan Baka

    Tsakure

    Burin wannan bincike lalubo wani salo daga cikin salailai da mawaƙan baka ke amfani da su wajen isar da saƙonsu ga masu sauraron su. An yi wa binciken take “Salon Sakaɗe: an ƙago sunan ne bisa ga tunanin magabatanmu masana ilmin waƙa. An ɗora aikin a kan mazhabar Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo na cikin Gadon Feɗe Waƙa da Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. An yi bitar karatun fitaccen aikin salo na Farfesa Abdullahi Bayero Yahaya mai taken: Salo Asirin Waƙa. An lalubi ayyukan masana da manazarta waƙa kimani talatin (30), an saurari waƙoƙin baka da dama don tantance bagiren bincike. An fasalta aikin cikin fasaloli goma sha bakwai (17) haɗa da gabatarwa da naɗewa. Bincike ya gano babu wani masani da ya sa kai kan “Salon Sakaɗe”; kuma babu wani aiki da aka gabatar a kan kowane mataki kan “sakaɗe”. Ganin dukkanin fitattun masana adabin waƙa, ba su ambace shi ba, ba kasawa ba ce, domin ba ya daga cikin fitattun salailai da aka ambata a waƙoƙin Ingilishi da na Larabci. Don haka, na gayyato ɗiyan waƙoƙi ashirin (20) cikin shahararrun waƙoƙin shahararrun makaɗa goma (10) na Hausa. Ga bincikena na tattaro misalai fiye da hamsin (50) amma na ga suna hawa matakai shida (6) na nazarin “Sakaɗe”. An yi yunƙurin fayyace kalmar “Sakaɗe” a luga da ilmin adabi. An kakkawo dalilan bayyanarsa a waƙa da muhalinsa da amfanoninsa da masu yin sa da yadda ake sarrafa shi. Binciken ya gano cikin kowane rukunin mawaƙa ana samun bayyanar salon in ban da mawaƙan da ke waƙa su kaɗai babu ‘yan amshi waɗanda binciken ya yi wa suna kai-kaɗai-gayya. Babu wai, “Sakaɗe” salo ne mai cin gashin kansa, wanda ya cancanci a saka shi cikin salailan da za a nazari a waƙoƙin baka. Dalili kuwa shi ne, yana da rassa biyar (5) masu ma’ana a nazarin salo.

    DOI: www.doi.org/10.36349/zwjohps.2025.v04i02.001

    author/Aliyu Muhammadu Bunza

    journal/Zauren Waƙa 4(2) | July 2025 |

    Pages